*"Kauna Ba Ta Gajiya"*
Kauna ba ita ce dariya kawai ba,
Ita ce riΖon hannu lokacin da iska ta yi sanyi.
Ita ce jimrewa idan jarab ta zo,
Ita ce addu'a a asirce, don Yan,uwa
**
Kauna ne hasken rayuwa
Idan Babu kauna rayuwa bazai Yi mana dadi ba
Kauna ba ta tambayar "me ka ba ni?"
Amma tana tambayar "yaya ka ke yau?"
Ba ta gudu lokacin jaraba ba,
Tana tsayuwa ta ce "Allah ya kyauta".
**
Kauna ne hasken rayuwa
Idan Babu kauna rayuwa bazai Yi mana dadi ba
Idan duniya ta kimu
Kauna ta zama gida mai laushi.
Idan kowa ya juya baya,
Kauna ta ce "ni nan nake da kai".
**
Kauna ne hasken rayuwa
Idan Babu kauna rayuwa bazai Yi mana dadi ba
Kauna bata yin kishi
Kauna bata kumbura
Kauna bata yin farinciki da mugunta
Kauna tana yafe laifofi da yawa
**
Kauna ne hasken rayuwa
Idan Babu kauna rayuwa bazai Yi mana dadi ba
Ina kaunar da baki ba shi ne kauna ba
Amman ka taimaka a lokacin wahala
Komai zai shude Amman kauna ba ta karewa
**
Kauna ne hasken rayuwa
Idan Babu kauna rayuwa bazai Yi mana dadi ba
**
Kauna ne hasken rayuwa
Idan Babu kauna rayuwa bazai Yi mana dadi ba
Kauna bata gajiya
Daga John G.o Arose