Yesu ka kawasda iyawa ta
**
Yesu ka kawasda iyawa ta
a cikin kowane abin da ni ke yi
Barin yi nufin ka kadai,
ya kasance a al'amura na
Na iya gudu, amma ban san buya ba
Ni makaho ne, kai ne mai gani
Yesu ka boye ni, a gicciyen ka
**
Yesu ka kawasda iyawa ta
a cikin kowane abin da ni ke yi
Barin yi nufin ka kadai,
ya kasance a al'amura na
Guguwa ta taso, zakoki sun bude baki
Ina neman wurin boya, ban san wurin ba
Yesu ka boye ni, a gicciyen ka
**
Yesu ka kawasda iyawa ta
a cikin kowane abin da ni ke yi
Barin yi nufin ka kadai,
ya kasance a al'amura na
Ni mai zunubi ne, na gaji da zunubi,
Yanzu ina son rabuwa da zunubi
Ban san yadda zan yi ba ya Ubangiji
**
Yesu ka kawasda iyawa ta
a cikin kowane abin da ni ke yi
Barin yi nufin ka kadai,
ya kasance a al'amura na
Abin da ni ke yi, ba shi ni ke so ba
Abin da ni ke so, ba shi ni ke yi ba
Ina kuka
Yesu ka boye ni, a gicciyen ka
**
Yesu ka kawasda iyawa ta
a cikin kowane abin da ni ke yi
Barin yi nufin ka kadai,
ya kasance a al'amura na
**
Yesu ka kawasda iyawa ta
a cikin kowane abin da ni ke yi
Barin yi nufin ka kadai,
ya kasance a al'amura na
Ni ma John G.o Arose,
Ka kawasda iyawa ta