Makaho ba ya Jan makaho gora
**
Ka cire hakki a idon ka kafin ka cire na wani
Laifi tudu ne, saika hau naka kafin ka gan na wani
Misali, makaho ba ya Jan makaho gora

Kada ka duba laifin dan'uwanka
Kowa da nasa ragon a wuyansa
Ubangiji ne kadai ke bamu iko
Ya wanke mu da jinin sa mai tsarki
**
Ka cire hakki a idon ka kafin ka cire na wani
Laifi tudu ne, saika hau naka kafin ka gan na wani
Misali, makaho ba ya Jan makaho gora
Dan uwa Ka gyara naka tukunan
Ka cire gungume a idanunka tukunan
Yadda zaka iya ganin na wani
**
Ka cire hakki a idon ka kafin ka cire na wani
Laifi tudu ne, saika hau naka kafin ka gan na wani
Misali, makaho ba ya Jan makaho gora
Ina zagi, Kai kuma kana gulma
Ina shan giya, Kai kuma kana sata
Yanzu, Ni da Kai wazai gyara Wani
**
Ka cire hakki a idon ka kafin ka cire na wani
Laifi tudu ne, saika hau naka kafin ka gan na wani
Misali, makaho ba ya Jan makaho gora
Zunubi, zunubi ne, Allah baya son zunubi
Babu Karamin zunubi ko babba
Yan uwana kowa ya tuba
**
Ka cire hakki a idon ka kafin ka cire na wani
Laifi tudu ne, saika hau naka kafin ka gan na wani
Misali, makaho ba ya Jan makaho gora
Mu tuba mu daina ganin laifi juna
Yesu yana zuwa, zai zo da sakamako
Wasu zasu karba da hawaye
**
Ka cire hakki a idon ka kafin ka cire na wani
Laifi tudu ne, saika hau naka kafin ka gan na wani
Misali, makaho ba ya Jan makaho gora
**
Ka cire hakki a idon ka kafin ka cire na wani
Laifi tudu ne, saika hau naka kafin ka gan na wani
Misali, makaho ba ya Jan makaho gora
Na gode
Gargadi daga John G.o Arose