1. Na ji kiranka yanzu, ya Ubangijina.
A cikin jininka, Yesu, ka wanke zuciyata.
Chorus
Ubangijina, ga ni nan, na zo,
Sai ka ji addu'ata, ka ba ni taimako.
2. Ko na zo da zunubi, da rashin ƙarfina,
Na sani kai ba za ka ƙi ka tsarkake ni ba.
Chorus
Ubangijina, ga ni nan, na zo,
Sai ka ji addu'ata, ka ba ni taimako.
3. A wurinka kaɗai akwai murna sosai.
Kai ne ka ba ni kwanciyar rai da sanin gaskiya.
Chorus
Ubangijina, ga ni nan, na zo,
Sai ka ji addu'ata, ka ba ni taimako.
4) Ina so in ci gaba, in zama cikakke,
In koyi irin halinka, in ɗauki giciye.
CHORUS
Ubangijina, ga ni nan, na zo,
Sai ka ji addu'ata, ka ba ni taimako.