Frobits
🎵 A song made on Frobits

Yesu Mai Cetona

0:000:00
Download
Reply with a song
Lyrics

1) Ubangiji, ka bishe ni
A tafiyata duka.
Sai ka ba ni farinciki,
Sai ka ba ni bangaskiya,
Sai ka yi mini alheri,
Sai ka taimake ni yau,
Gama ni ban iya kome,
Ni kaɗai, a duniya ba.
2) Ubangiji, ka bishe ni
A tafiyata duka,
Gama a kan jarabce ni,
Ni kan shiga tsanani
Duk wahala daga Shaiɗan
Ta kan dulmayad da ni
Gama ni ban iya kome,
Ni kaɗai, a duniya ba.
3) Ubangiji, ka bishe ni
A tafiyata duka,
Gama ilmi ya kan kasa,
Ina son hikimarka.
Duk ƙoƙarina ya kasa,
Sai ka ba ni ƙarfinka
Gama ni ban iya kome,
Ni kaɗai, a duniya ba.
4) Ubangiji, ka bishe ni
A tafiyata duka,
Kuma ranar da zan mutu,
Sai ka yi ta taimako.
Ina so in yi ta shiri
Don in tsaya gabanka.
Ni kaɗai ban iya zuwa
Cikin kwarin mutuwa ba,
Ni kaɗai ban iya zuwa
Cikin kwarin mutuwa ba.

More songs by Godiya Listen to songs created by others
FROBITS